Yaren Chakali

Yaren Chakali
Lamban rijistar harshe
ISO 639-3 cli
Glottolog chak1271[1]

Chakali (tʃàkálɪ́ɪ́) yaren Gur ne na Ghana, kusan mutane 3,500 ke magana a ƙauyuka da yawa a gundumar Wa Gabas ta Babban Yamma . Musamman ma, mazauna kauyukan Tiisa, Sogla, Tousa, Motigu, Ducie, Katua da Gurumbele suna magana da Chakali. Yawancin masu magana da Chakali kuma suna magana da Wali ko Bulengi. Wasu na ganin cewa ba da jimawa ba harshen Chakali zai ƙare, inda Wali da Bulengi za su zama harsunan da za a yi amfani da su a ƙauyukan.

  1. Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Yaren Chakali". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy